LABARI MAI DADI GA TALAKAWAN NAJERIYA
- Shugaban kasa Bola Tinubu, ya rubutawa majalisar wakilai wasika yana neman ta amince mishi domin ya rabawa ‘yan Najeriya Naira biliyan 500 domin rage musu radadin halin da suka shiga kan cire tallafin Man Fetur.

A zaman majalisa na yaune kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta wasikar shugaban kasar a zauren majalisar. Idan suka amince da wannan kudirin tabbas talakawan Najeriya zasu amfana musamman idan aka bi tsarin tsohuwar Gwamnati.
Fatanmu Allah yasa wannan kudirin ya tabbata, Allah yasa duk wa ‘yanda suke da alhaki akan Approval din su amince da wuri.